Yaushe Nura zai yi Aure? Tambbayar da akasarin mutane ke yi kenan akan wannan fittacen mawaki. To ga dukkan alamu wannan lokaci fa ya riga ya karaso domin kuwa a ranar Asabar din nan Wanda ta yi daidai da 29 ga watan April 2017 za a daura auren wannan fittacen mawaki da Amaryarsa Amina a garin Katsina, Sai dai kafin daurin Auren za a gudanar da wasan kwallon kafa da kuma dinner a ranar 27 da 28. Kamar yadda mu ka samo labari akwai albam guda da mawakin ya shirya na wannan aure na sa da yayi wa lakabi ranar Aurena' ana tunanin zai saki albam din a sallah karama. to sai mu ce Allah ya ba da zaman lafiya, Amin. Written by Garkuwa Twitter/Instagram: @garkuwaofficial WhatsApp: 08090503169