Written by: Garkuwa , Friday 27 -10- 2017. Ga dukkan alamu akwai yiwuwar hukumar MOPPAN za ta warware hukuncin kora kwata kwata ga jarumar fina finai Rahama Sadau bayan da a ranar 25 ga watan nan jarumar ta fito fili ta shelanta ban hakuri da Neman afuwa ga MOPPAN da kuma duk wanda al'amarin fitowarta a wakar #iloveyou ya bakantawa. Sannan an ga hotunan ziyara da Ali nuhu da yaseen Auwal da kuma Rahama Sadau da su ka kaiwa darakta Na hukumar tace fina finai Malam isma'il Afakalla wanda ake ganin duka wannan na daga cikin yunkuri na dawo da wannan jaruma. Abu ne mai kyau a yafewa wannan jaruma, domin Allah ma ya na yafewa bawa idan har ya cika sharuddan tuba, Akwai yiwuwar kwamitin MOPPAN da a yanzu haka suke zaman yanke tattaunawa akan wannan batu su fitar da sakamako mai kyau na yafewa wannan jaruma laifin da ta aikata. #rahamasadau #alinuhu @yaseenauwal #sadaupictures #bbchausa @daily_trust #MOPPAN