Skip to main content

Posts

ZA A JANYE DAKATAR DA RAHAMA SADAU DAGA FIM

Written by: Garkuwa , Friday 27 -10- 2017. Ga dukkan alamu akwai yiwuwar hukumar MOPPAN za ta warware hukuncin kora kwata kwata ga jarumar fina finai Rahama Sadau bayan da a ranar 25 ga watan nan jarumar ta fito fili ta shelanta ban hakuri da Neman afuwa ga MOPPAN da kuma duk wanda al'amarin fitowarta a wakar #iloveyou ya bakantawa. Sannan an ga hotunan ziyara da Ali nuhu da yaseen Auwal da kuma Rahama Sadau da su ka kaiwa darakta Na hukumar tace fina finai Malam isma'il Afakalla wanda ake ganin duka wannan na daga cikin yunkuri na dawo da wannan jaruma. Abu ne mai kyau a yafewa wannan jaruma, domin Allah ma ya na yafewa bawa idan har ya cika sharuddan tuba, Akwai yiwuwar kwamitin MOPPAN da a yanzu haka suke zaman yanke tattaunawa akan wannan batu su fitar da sakamako mai kyau na yafewa wannan jaruma laifin da ta aikata. #rahamasadau #alinuhu @yaseenauwal #sadaupictures #bbchausa @daily_trust #MOPPAN
Recent posts

Hotunan bikin nada Ali Artwork sarkin barkwancin kasar hausa

.

Ranar Aurena by Nura M. inuwa| Garkuwa Tv

Yadda na ji rauni a fim din Dakin Amarya —Aisha Tsamiya Source @ bbchausa Fitacciyar jarumar nan ta fina-finan Kannywood, Aisha Aliyu, wacce aka fi sani da suna Aisha Tsamiya ta shaida wa BBC cewa babu fim din da ya taba ba ta wahala kamar "Dakin Amarya". Fim din Dakin Amarya yana magana ne kan yadda mata ke bakin kishi, musamman idan aka auro musu abokiyar zama - ta fito ne a matsayin kishiyar Halima Atete, wacce ita ce uwar gidan Ali Nuhu. "Sai da na ji rauni na gaske a fim din musamman saboda yadda aka rika yin fatali da kayan daki irinsu tangaran da talabijin", in ji Aisha Tsamiya, a hirar da ta yi da Nasidi Adamu Yahaya. Jarumar ta kara da cewa tun tana karama take sha'awar fitowa a fina-finan Kannywood "saboda suna matukar burge ni". A cewarta, "Na dauki yin fim a matsayin sana'a don haka ina jin dadin fitowa a cikinsa." Tsamiya, wacce ta soma fim a shekarar 2011, ta kara da cewa dukkan jaruman da ke yin fim tare da ita suna...
ADAM ZANGO ZAI CHANZA KANNYWOOD DA FIM DIN GWASKA. Gogarman jarumin fina finai Adam A Zango ya kama hanyar  kawo wani gagarumin sauyi a harkar fina finai ba ga Kannywood kawai ba ga dukkan masana'antar fina  finan afirka da fim dinsa #gwaskareturns. #gwaskreturns fim  ne  da ba a taba ganin tsaransa ba a tarihin fina finai a najeriya, Fim  ne  da ya mori  labari, hoto, Ingantaccen aiki, da kuma siddabaru na zamani da mu ka saba ganinsu a manyan masana'antun da suka cigaba irinsu #Hollywood #bollywood da dai sauransu. Sau  tari akwai fina finai da mu ka ji an yayata cewa an kashe musu makudan kudi lokacin shiryawa , sai dai irin wadanchan fina finai idan ka kalle su za ka ga babu gurbin inda aka kashe wannan kudaden da aka fada , To amma game da fim din #Gwaskareturns ba ka bukatar sai an fada maka fim  din ya kwamushe miliyoyin nairori alokacin shirya shi. An shirya za a haska wannan gagarumin fim a ranar babbar sallah a many...

Ango Ali dawayya da Amaryarsa