Skip to main content
ADAM ZANGO ZAI CHANZA KANNYWOOD DA FIM DIN GWASKA.

Gogarman jarumin fina finai Adam A Zango ya kama hanyar  kawo wani gagarumin sauyi a harkar fina finai ba ga Kannywood kawai ba ga dukkan masana'antar fina  finan afirka da fim dinsa #gwaskareturns.

#gwaskreturns fim  ne  da ba a taba ganin tsaransa ba a tarihin fina finai a najeriya, Fim  ne  da ya mori  labari, hoto, Ingantaccen aiki, da kuma siddabaru na zamani da mu ka saba ganinsu a manyan masana'antun da suka cigaba irinsu #Hollywood #bollywood da dai sauransu.

Sau  tari akwai fina finai da mu ka ji an yayata cewa an kashe musu makudan kudi lokacin shiryawa , sai dai irin wadanchan fina finai idan ka kalle su za ka ga babu gurbin inda aka kashe wannan kudaden da aka fada , To amma game da fim din #Gwaskareturns ba ka bukatar sai an fada maka fim  din ya kwamushe miliyoyin nairori alokacin shirya shi.

An shirya za a haska wannan gagarumin fim a ranar babbar sallah a manyan  sinima a fadin  wasu  jahohin arewacin najeriya da su ka hada  da Kano, Kaduna , Abuja, Katsina , Sokoto , Zamfara , Adamawa , Sannan kuma da wa su jahohin jamhuriyar Nijar.

#film #cinema #kano #katsina #zamfara #niamey #niger #kaduna #abuja #action #actionfilm #actress #director #producer #africa #nigeria #entertainment  #adamazango #adamzango #gwaskareturns #gwaskareturn @adam_azango

Comments

Popular posts from this blog

Ba Zan Dawo Fim ba sai na Kammala karatuna-

Naja'atu ta fara fim tun tana shekaru goma, Da fim din Murjanatu yar baba,  Shekaru bakwai baya. Shekarun baya ta dawo ta yi wa su fina finai daga  nan sai aka jita shiru. Fimhausa Media mun tattauna da ita ga yadda hirar ta kasance. FIMHAUSA: Da farko za mu fara jin cikakken sunanki da takaitaccen tarihinki?  NAJA'ATU: Suna na Naja'atu mohd Suleiman. An haifeni a garin kano Shekaru na 17 na kammala Secondary school di na. Ina Northwest university yanxu level One.  FIMHAUSA: Yaushe ki ka fara fim ki na shekara nawa?  NAJA'ATU:  Ina shekara 10 na fara film lokacin na gama primary school.  FIMHAUSA : Wanne fim ne?  NAJA'ATU :  Film din na na farko shine Murjanatu yar baba.  FIMHAUSA : Dama ki na sha'awar fim ne alokacin ke kike son yi ko gidan ku ne? NAJA'ATU :  No gaskiya Ina sha'awar yi Sai na fada a gidan Sai aka amince.  FIMHAUSA : Ta hannun wa ki ka shiga?  NAJA'ATU :  Ta hannun darakta Ashiru Nagoma  FIMHAUS...

ADAM A. ZANGO to release gwaska return trailer on August 12.

The kannywood @adam_a_zango decided to unveil the trailer  in kano state, the second largest city in Nigeria where the film industry is mainly based. #kannywood #film #movie #trailer #nigerianfilm #actor #director #producer

Nura M Inuwa zai Angwance | Zai fitar da Albam na musamman

Yaushe Nura zai yi Aure? Tambbayar da akasarin mutane ke yi kenan akan wannan fittacen mawaki. To ga dukkan alamu wannan lokaci fa ya riga ya karaso domin kuwa a ranar Asabar din nan Wanda ta yi daidai da 29 ga watan April 2017 za a daura auren wannan fittacen mawaki da Amaryarsa Amina a garin Katsina, Sai dai kafin daurin Auren za a gudanar da wasan kwallon kafa da kuma dinner a ranar 27 da 28. Kamar yadda mu ka samo labari akwai albam guda da mawakin ya shirya na wannan aure na sa da yayi wa lakabi ranar Aurena' ana tunanin zai saki albam din a sallah karama. to sai mu ce Allah ya ba da zaman lafiya, Amin. Written by Garkuwa Twitter/Instagram: @garkuwaofficial WhatsApp: 08090503169