Naja'atu ta fara fim tun tana shekaru goma, Da fim din Murjanatu yar baba, Shekaru bakwai baya. Shekarun baya ta dawo ta yi wa su fina finai daga nan sai aka jita shiru. Fimhausa Media mun tattauna da ita ga yadda hirar ta kasance.
FIMHAUSA: Da farko za mu fara jin cikakken sunanki da takaitaccen tarihinki? NAJA'ATU: Suna na Naja'atu mohd Suleiman. An haifeni a garin kano Shekaru na 17 na kammala Secondary school di na. Ina Northwest university yanxu level One. FIMHAUSA: Yaushe ki ka fara fim ki na shekara nawa? NAJA'ATU: Ina shekara 10 na fara film lokacin na gama primary school. FIMHAUSA : Wanne fim ne? NAJA'ATU : Film din na na farko shine Murjanatu yar baba. FIMHAUSA : Dama ki na sha'awar fim ne alokacin ke kike son yi ko gidan ku ne? NAJA'ATU : No gaskiya Ina sha'awar yi Sai na fada a gidan Sai aka amince. FIMHAUSA : Ta hannun wa ki ka shiga? NAJA'ATU : Ta hannun darakta Ashiru Nagoma FIMHAUSA : Bayan fim din murjanatu yar baba kin yi fina finai nawa? NAJA'ATU : guda biyar ne akwai Harira, Auren Gaja, Hakkin Rai, Murjanatu.
FIMHAUSA : Yanzu ba a ganinki sosai me yasa NAJA'ATU : A gaskiya yanzu ba na fim sai na kammala karatuna. FIMHAUSA : Cikin fina-finan da kika yi wanne kika fi so? NAJA'ATU : Gaskiya na fi son murjanatu Saboda na samu roll Mai kyau koma nayi achiven Dream di na. Kuma film din Mutane sun so shi sosai. Kuma dama film Ana yin shi ne don al'umma. FIMHAUSA : Kafin ki yi fim din kun san juna da Amude booth da ku ka yi fim din da shi? NAJA'ATU : Aa bamu san juna ba alokacin. FIMHAUSA : Bayan fim din murjanatu yar baba alakar ku ta cigaba da shi ko kun rabu? NAJA'ATU : Gaskiya alakar mu ta cigaba mun zama kaman family friends. FIMHAUSA : Wanne jarumi ki ka fi so NAJA'ATU : Kowa ya na burgeni amma Ali Nuhu da Adam A. Zango sun fi burgeni, A mata kuma Hadiza gabon da rahama. FIMHAUSA : kamar wa kike so ki zama nan gaba? NAJA'ATU : Bana son in zama kamar kowa Ina son in zama kamar kaii nah.
FIMHAUSA: Daga karshe akwai masoyanki da su ke son su rika ganinki a fim, Wanne albishir za ki musu na dawowar ki bayan kammala karatu.
NAJA'ATU : Duk masoya na masu son in dawo film Ina so sumun aduo'a Allah ya zaba mun abun da yafi Alkairi . Koma Ina fatan in na gama makaranta zasu ganni insha Allah.
Follow us on Twitter/instagram: @FIMHAUSA WHATSAPP: 08090503169 #BBM : 592E5211
Allah bada sa'a
ReplyDeleteAllah yasamunadarabunganin wananlokacin ameem summa ameen
ReplyDeleteNice post. Thanks for sharing this. Commercial Painters Sydney
ReplyDelete