Skip to main content

Ba Zan Dawo Fim ba sai na Kammala karatuna-

Naja'atu ta fara fim tun tana shekaru goma, Da fim din Murjanatu yar baba,  Shekaru bakwai baya. Shekarun baya ta dawo ta yi wa su fina finai daga  nan sai aka jita shiru. Fimhausa Media mun tattauna da ita ga yadda hirar ta kasance.

FIMHAUSA: Da farko za mu fara jin cikakken sunanki da takaitaccen tarihinki?  NAJA'ATU: Suna na Naja'atu mohd Suleiman. An haifeni a garin kano Shekaru na 17 na kammala Secondary school di na. Ina Northwest university yanxu level One.  FIMHAUSA: Yaushe ki ka fara fim ki na shekara nawa?  NAJA'ATU:  Ina shekara 10 na fara film lokacin na gama primary school.  FIMHAUSA : Wanne fim ne?  NAJA'ATU :  Film din na na farko shine Murjanatu yar baba.  FIMHAUSA : Dama ki na sha'awar fim ne alokacin ke kike son yi ko gidan ku ne? NAJA'ATU :  No gaskiya Ina sha'awar yi Sai na fada a gidan Sai aka amince.  FIMHAUSA : Ta hannun wa ki ka shiga?  NAJA'ATU :  Ta hannun darakta Ashiru Nagoma  FIMHAUSA : Bayan fim din murjanatu yar baba kin yi fina finai nawa?  NAJA'ATU : guda biyar ne akwai Harira, Auren Gaja, Hakkin Rai, Murjanatu.

FIMHAUSA : Yanzu ba a ganinki sosai me yasa NAJA'ATU : A gaskiya yanzu ba na fim sai na kammala karatuna. FIMHAUSA :  Cikin fina-finan da kika yi wanne kika fi so?  NAJA'ATU : Gaskiya na fi son murjanatu  Saboda na samu roll Mai kyau koma nayi achiven Dream di na. Kuma film din Mutane sun so shi sosai. Kuma dama film Ana yin shi ne don  al'umma.  FIMHAUSA :  Kafin ki yi fim din kun san juna da Amude booth da ku ka yi fim din da shi?  NAJA'ATU : Aa bamu san juna ba alokacin.  FIMHAUSA :  Bayan fim din murjanatu yar baba alakar ku ta cigaba da shi ko kun rabu?  NAJA'ATU : Gaskiya alakar mu ta cigaba mun zama kaman family friends. FIMHAUSA : Wanne jarumi ki ka fi so NAJA'ATU : Kowa ya na burgeni amma Ali Nuhu da Adam A. Zango sun fi burgeni, A mata kuma Hadiza gabon da rahama. FIMHAUSA : kamar wa kike so ki zama nan gaba?  NAJA'ATU :  Bana son in zama kamar kowa Ina son in zama kamar kaii nah󾰀󾌴󾌴.
FIMHAUSA:  Daga karshe akwai masoyanki da su ke son su rika ganinki a fim, Wanne albishir za ki musu na dawowar ki bayan kammala karatu.
NAJA'ATU : Duk masoya na masu son in dawo film Ina so sumun aduo'a Allah ya zaba mun abun da yafi Alkairi . Koma Ina fatan in na gama makaranta zasu ganni insha Allah.

Follow us on Twitter/instagram: @FIMHAUSA   WHATSAPP: 08090503169 #BBM : 592E5211

Comments

Post a Comment

Popular posts from this blog

ADAM A. ZANGO to release gwaska return trailer on August 12.

The kannywood @adam_a_zango decided to unveil the trailer  in kano state, the second largest city in Nigeria where the film industry is mainly based. #kannywood #film #movie #trailer #nigerianfilm #actor #director #producer

Nura M Inuwa zai Angwance | Zai fitar da Albam na musamman

Yaushe Nura zai yi Aure? Tambbayar da akasarin mutane ke yi kenan akan wannan fittacen mawaki. To ga dukkan alamu wannan lokaci fa ya riga ya karaso domin kuwa a ranar Asabar din nan Wanda ta yi daidai da 29 ga watan April 2017 za a daura auren wannan fittacen mawaki da Amaryarsa Amina a garin Katsina, Sai dai kafin daurin Auren za a gudanar da wasan kwallon kafa da kuma dinner a ranar 27 da 28. Kamar yadda mu ka samo labari akwai albam guda da mawakin ya shirya na wannan aure na sa da yayi wa lakabi ranar Aurena' ana tunanin zai saki albam din a sallah karama. to sai mu ce Allah ya ba da zaman lafiya, Amin. Written by Garkuwa Twitter/Instagram: @garkuwaofficial WhatsApp: 08090503169