Skip to main content

Posts

Showing posts from February, 2017

KURA - KURAI DA AKA YI AKAN MATAKAN LADAFTAR DA RAHAMA SADAU.

Nasan wani zai ce na danna tariyar baya akan Al'amarin da ya fara zama tsohon zance to Amma fa hausawa kan ce waiwaye adon tafiya. Zan so ku fuskanci ba ina nufin Rahama Sadau ba ta yi laifi ba ne,  A'a! Ina nufin matakan da aka bi wajen hukunta ta ba ayi su kan ka'ida ba. DALILAI A lokacin da bidiyon da aka hukunta Rahama Sadau ya fito,  ita Rahaman ba ta najeriya ta na India,  a ka'ida ya kamata a fara gayyatar Rahama ta zo ta kare kanta,  Amma ba a jira hakan ba aka yanke hukunci a gaggauce kuskure na farko kenan! Abu na biyu kundin tsarin mulkin kungiyar ma su shirya fina finai (in ma akwai shi) ba bu inda yayi bayanin inda za a kori mutum kwata - kwata. Abu na uku na karshe da zan yi magana akai shine hukuncin kora kwata - kwata ya yi tsamari duk da Rahama Sadau ta yi laifi to Amma hukuncin an yi shi da tsauri. Idan Rahama Sadau ta maka kungiyar ma su shirya fina finai a kotu ba na tunanin ba za ta kada su ba,  saboda ai kungiya ce idan kungiya ta karya d...