Skip to main content

Posts

Showing posts from November, 2015

ADAM ZANGO DA RAHAMA SADAU NE SUKA LASHE GWARAZAN AFRICAN VOICE AWARD

An kammala African Voice award lafiya a kasar landan inda aka bayyana wadanda su ka samu nasara a fafatawar: ADAM A. ZANGO an karrama shi a matsayin gwarzon jarumin jarumai. RAHAMA SADAU: an karrama ta a matsayin gwarzuwar jarumar jarumai. HAFIZU BELLO: an karrama shi a matsayin daraktan daraktochi. ALI NUHU an karrama shi saboda karfafawa matasa a masana'antar fina-finan hausa. Mu na taya su murna Allah ya dawo da su lafiya  Marubuci: @garkuwa_

Ba Zan Dawo Fim ba sai na Kammala karatuna-

Naja'atu ta fara fim tun tana shekaru goma, Da fim din Murjanatu yar baba,  Shekaru bakwai baya. Shekarun baya ta dawo ta yi wa su fina finai daga  nan sai aka jita shiru. Fimhausa Media mun tattauna da ita ga yadda hirar ta kasance. FIMHAUSA: Da farko za mu fara jin cikakken sunanki da takaitaccen tarihinki?  NAJA'ATU: Suna na Naja'atu mohd Suleiman. An haifeni a garin kano Shekaru na 17 na kammala Secondary school di na. Ina Northwest university yanxu level One.  FIMHAUSA: Yaushe ki ka fara fim ki na shekara nawa?  NAJA'ATU:  Ina shekara 10 na fara film lokacin na gama primary school.  FIMHAUSA : Wanne fim ne?  NAJA'ATU :  Film din na na farko shine Murjanatu yar baba.  FIMHAUSA : Dama ki na sha'awar fim ne alokacin ke kike son yi ko gidan ku ne? NAJA'ATU :  No gaskiya Ina sha'awar yi Sai na fada a gidan Sai aka amince.  FIMHAUSA : Ta hannun wa ki ka shiga?  NAJA'ATU :  Ta hannun darakta Ashiru Nagoma  FIMHAUS...