Skip to main content

Posts

Showing posts from March, 2017

JARUMI ALI NUHU ZAI CIKA SHEKARA 43 A DUNIYA , 18 A KANNYWOOD.

Fittacen jarumin fina finan hausa Ali Nuhu zai cika shekaru 43 a duniya a ranar larabar nan. An haifi jarumin a shekarar 1974 ya fara harkar fina finai a 1999 shekaru 18 kenan da su ka gabata, Wannan ya nuna Ali Nuhu a matsayin jarumin da ya fi dadewa ya na jan zarensa a masana'antar ta fina finai da aka fi sani da kannywood. Idan aka yi la'akari da takwarorin Ali Nuhu a duniya irinsu Amirkhahn mai shekaru 51 aduniya da kuma shahrukhhahn shima shekara 51 Amma har yanzu ana damawa da su,  Idan mu ka yi la 'akari da wannan a shekaru 43 na jarumi Ali Nuhu hakan na nuni da cewa akwai  sauran tafiya akwai dumbin gudunmawa da zai cigaba da bayarwa zuwa lokaci mai tsawo a gaba.

Yadda shari'a tsakanin mawaki sadiq zazzabi ta kaya da gwamnatin jahar kano.

A yau ne aka saurari shari'ar da ta yi matukar farin jini gami da daukar hankalin dubun dubatar mutane tsakanin mawaki Sadiq zazzabi da kuma gwamnatin jahar kano. A zaman na yau alkalin da ke sauraren shari'ar ya amince da bayar da belin wannan mawaki bisa wadansu sharudda da aka gindaya, Wanda tuni aka cika su an kuma saki mawakin har zuwa lokacin da za a dawo a cigaba da sauraron ba'asi. In za ku tuna dai gwamnatin jahar kano ce ta kama gami da garkame wannan mawaki bisa zarginsa da fitar da wata waka da ya rairawa tsohon gwamnan jahar kano Rabi'u kwankwaso ba tare da an bashi izini ba. yau ne aka saurari shari'ar da ta yi matukar farin jini gami da daukar hankalin dubun dubatar mutane tsakanin mawaki Sadiq zazzabi da kuma gwamnatin jahar kano.

Nazifi Asnanic da sauran mawaka sun yi zanga zanga akan kama Sadiq Zazzabi

Mawakan kannywood irin Su Nazifi Asnanic da Ali jita sun yi zanga zanga a Kafofin sadarwa na Instagram inda Su Ka nemi da a gaggauta sakin mawakin nan da gwamnatin jahar kano ta tsare. Idan za Ku tuna dai gwamnatin jahar kanon ta kama da kuma tsare mawaki Sadiq zazzabi gami da maka shi a kotu bisa zargin sa da fitar da wakarsa da ya rairawa tsohon gwamnan jahar Rabi'u kwankwaso Ba tare da an Ba shi izinin fitarwa a hukumance Ba.

Hotunan shagalin sunan Alamin Abdul Amart Mai kwashewa

A wannan makon ne aka yi walimar radin sunan dan farko da produsa Abdul Amart ya samu. Yan fim da dama ne suka halarci walimar ga hotunan wainar da aka toya .